Majalisar Amurka ta amincewa dokar banki

Shugaba Obama na Amurka
Image caption Amincewa da wannan doka babbar nasara ce ga Shugaba Barack Obama

Majalisar Dattawan Amurka ta kada kuri'ar amincewa da wata doka wadda za ta yi garambawul ga harkokin banki a kasar.

Wannan wata gagarumar nasara ce dai ga Shugaba Obama, wanda ya dauki yin gyaran fuska ga harkokin hada-hadar kudade daya daga cikin muhimman manufofin gwamnatinsa.

An dai bayyana dokar da cewa ita ce matakin garambawul ga harkokin banki a Amurka mafi girma tun bayan gagarumin koma-bayan tattalin arzikin da kasar ta fuskanta a shekarun 1930.

'Yan Majalisar Dattawan na Amurka hamsin da tara ne dai suka goyi bayan amincewa da wannan doka yayin da talatin da tara suka ki amincewa.

Da wannan ne kuma hankulan 'yan siyasa daga jam'iyyar Democrat ta Shugaba Obama za su kwanta, kasancewar bangarori biyu na Majalisar Dokokin Amurkan sun amince da dokar, duk kuwa da yunkurin da Shugaba Obaman ya ce manyan bankunan kasar sun yi na yiwa dokar kafar ungulu.

Dokar dai ta tanadi cewa bankunan su yi shamaki tsakanin ayyukansu na hada-hadar yau da kullum da kuma kasuwancin da suke yi wanda ke cike da kasada.

Dokar ta kuma tanadi kirkiro wata hukuma mai zaman kanta wadda za ta sa ido a kan harkokin bankunan kasar.

Shugaba Obama ya yi alkawarin cewa da wannan ci gaba da aka samu, ba za a sake ba cibiyoyin hada-hadar kudade tallafi daga aljihun gwamnati ba.

“Saboda wannan garambawul a tsarin hada-hadar kudadenmu, ba za a sake ba cibiyoyin hada-hadar kudade tallafi da kudin al'umma ba.

“Duk wata cibiyar hada-hadar kudade da ta kasa nan gaba, muna da dabarun kai ta rami ba tare da jefa tattalin arzikinmu cikin hadari ba.

“Dadin dadawa kuma akwai dokokin da za su ma hana cibiyoyin hada-hadar kudaden tumbatsar da za ta sa su kasa yin katabus”, inji Mista Obama.

Sai dai 'yan jam'iyyar Republican din da suka kada kuri'ar kin amincewa da dokar sun yi ikirarin cewa dokar za ta dakile ci gaban tattalin arzikin kasar.