Birtaniya tace babu sabani akan Afghanistan

William Hague
Image caption Sakataren harkokin wajen Birtaniya William Hague

Wasu ministocin Birtaniya da ke ziyara a birnin Kabul, sun yi watsi da batun cewa, akwai alamun rarrabuwar kawuna game da irin rawar da Birtaniyar ke takawa a Afghanistan.

Sakataren harkokin wajen Birtaniyar, William Hague, ya ce hukumomin Afghanistan za su gano cewa, sabuwar gwamnatin Birtaniyar, kawa ce da za su iya dogara da ita. Amma ya ki ya tsayar da ranar janyewar dakarun Birtaniyar.

To sai dai a hirar da yayi da wata jarida kamin ziyarar a Afghanistan, sakataren tsaron Birtaniyar Liam Fox, ya ce yana son ganin sojojin Birtaniyar sun janye ba tare da bata lokaci ba.