Hadarin jirgi ya hallaka 160 a Indiya

Jirgin Air India da ya kama da wuta a Mangalore
Image caption Kusan mutane 160 ne suka rasa rayukansu a hadarin jirgin saman

Kusan mutane dari da sittin ne ake fargabar sun rasa rayukansu a wani hadarin jirgin saman kamfanin Air India a kudancin kasar Indiya.

Jirgin saman, kirar Boing 737, ya zarta hanyar saukar jiragen saman Mangalore mai cike da tsaunuka ne ya kuma daki wata katanga da ke iyakar filin jirgin saman sannan ya kama da wuta bayan ya ci karo da wani tsauni.

Wani jami'i a filin jirgin saman ya shaidawa BBC cewa a cikin fasinjoji fiye da dari da sittin din da ke cikin jirgin, ana fargabar shida ko bakwai ne kawai suka tsira da rayukansu.

Yawancin fasinjojin jirgin dai ma'aikata ne 'yan Indiya da ke aiki a yankin Tekun Fasha wadanda suka koma gida don ganin iyalansu.

An gina filin jirgin saman Mangalore ne dai a tsakanin tsaunuka, al'amarin da ya sanya ya ke da wuyar sha'ani ga matuka jiragen sama.

Hakazalika an yi kwanaki biyu ana tafka ruwan sama a yankin; kuma ko kafin jirgin ya yi kokarin sauka ma an yi ruwa.

Wannan ne dai hadarin jirgin sama na farko a cikin kusan shekaru goma a Indiya.