Mutane 7 sun tsira daga hadarin jirgin Indiya

Wanda ya tsira daga hadarin jirgin Indiya
Image caption Mutane 7 daga cikin pasinjoji 160 ne suka tsira daga hadarin jirgin saman Indiya

Rahotanni daga Indiya sun ce, mutane bakwai ne suka tsira da ransu, daga cikin pasinjoji 160 da ke cikin jirgin saman da yayi hadari da sanyin safiyar yau, a kudancin kasar.

Jirgin saman, kirar Boeing 737, na kamfanin Air India Express, ya taso ne daga Dubai. Ya kuma kama da wuta ne yayin da yake kokarin sauka a birnin Mangalore.

Mutanen da suka tsira sun ce sun ji babbar kara, kamar dai ta fashewar taya, jim kadan bayan da jirgin saman ya taba kasa.

Ministan Indiya mai kula da sufurin jiragen sama, ya kai ziyara a wurin da jirgin yayi hadari. Hukumomi sun fara gudanar da bincike domin gano musabbabin hadarin.