Mutane 6 sun hallaka a rikicin kabilanci a Jos

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, rahotanni daga jahar Plateau sunce an kashe akalla mutane 6, a tashin hankalin da aka yi a baya bayan nan, tsakanin Fulani da 'yan kabilar Birom.

Sojojin dake aikin wanzar da zaman lafiya a yankin sunce sun kama mutane 15 da ake zargin suna da hannu a rikicin.

A jiya Asabar ne tashin hankalin ya barke tsakanin Fulanin da Birom, a gundumar Fan dake Barikin ladi, inda aka kashe Fulani 3. A yau kuma an kashe mutane ukku a Jos, babban birnin jahar.

Gwamanatin Plateaun tace tana daukar matakan da suka kamata, yayin da ake cigaba da zaman zullumi.

Jahar Plateau dai ta sha fama da rikice rikicen dake da nasaba da addini da kabilanci a 'yan shekarun nan, wadanda suka janyo hallakar dubban jama'a da kuma hasarar dukiya mai yawa.