Iran ta nemi a yi musayar fursuna da Amirka

Fursunoni Amirkawa a Tehran
Image caption Fursunoni Amirkawa a Tehran

Kasar Iran ta nuna cewa, hukumomin Washington sun yi tayin yin musayar fursuna, domin ganin an sako wasu Amirkawa ukku da aka tsare a birnin Tehran, bisa zargin yin leken asiri.

Amirkawan dai sun ce sun shiga Iran ne bisa kuskure, yayin da suke tafiya a yankin arewacin Iraki a bara.

To amma hukumomin Iran sun sha yin biris da roke-roken da ake na neman a sako su.

Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amirka ya ce ba wata tattaunawar da aka yi tsakanin kasashen biyu, akan yiwuwar yin musayar fursuna, yana mai cewar ya kamata a saki Amirkawan ukku nan take.