An nada sabon shugaban hukumar zaben Jamhuriyar Nijar

Sojojin Nijar
Image caption Tunda sojoji suka karbi mulki suka yi alkawarin maida kasar tafarkin Demokradiyya

Hukomomin Jamhuriyar Nijar sun nada Malam Gousmane Abdourahamane a matsayin sabon shugaban hukumar zaben kasar mai lakabin CENI da faransanci.

Malam Gousmane Abdourahamane wanda kwarraren alkalin Magistarai ne, shi ne zai shirya zabukkan da ake saran yi a kasar a karshen wannan shekarar kafin wa'adin mikawa farar hula mulki a watan Maris na badi.

A wani zaman gaggawa wanda ya kunshi jam'iyyun siyasa hamsin da daya dake kasar, da kuma jami'an gwamnati ne aka zabi Mallam Gousmane a matsayin sabon shugaban hukumar ta CENI a jiya .

Alhaji Aliyu Abubakar wanda shi ne babban sakataren yada labaru na jamiyyar R-D-P jama'a ya fadama BBC cewa jamiyyar sa tayi marhaban da wannan zabe kasancewar jam'iyyun siyasar kasar ne suka zabe shi.

Sai dai wakilin BBC ya ce duk da amannar da hukumomin suka baiwa shugaban hukumar zaben da mukarrabansa, sai da aka sa suka yi rantsuwa domin bada tabbacin cewa za su yima `yan kasar adalci a lokacin zaben.