Nijer na neman a janye mata takunkumi

Shugaban Sojin Niger, Salou Djibo
Image caption Shugaban mulkin Sojin Niger, Salou Djibo

A jamhuriyar Nijer wata tawagar mambobin gwamnatin kasar a karkashin jagorancin Fira Minista, Dokta Mahammadu Danda ta isa birnin Brussels na kasar Belgium domin ganawa da majalisar tarayyar Turai .

A lokacin ziyarar dai, tawagar ta Nijer za ta baiwa kasashen tarayyar Turan tabbacin hukumomin mulkin sojan Nijer din da anniyar su ta shirya zabubbuka tare da maida mulki a hannun farar hula kafin ranar daya ga watan Maris na badi.

Haka kuma za ta nemi kungiyar tarayyar Turai da ta janye wani takunkumin tattalin arziki da siyasa da ta kakaba wa kasar ta Nijer.

Tun bayan da tsohuwar gwamnatin Malam Mamadou Tandja ta canza kundin tsarin mulki domin zarcewa kan karagar mulki ne dai, kasashen duniya da dama suka yi Allah wadai da kasar.

Abinda ya janyo wasu daga cikin su sanyawa kasar takunkumi, ciki har da tarayyar ta Turai.

Ko a makon da ya gabata, sai da babban bankin duniya ya sake kulla dangantaka da kasar, inda ya ba ta tallafin dala miliyan 400.