Asusun IMF ya bukaci Spain tayi sauyin tattalin arziki

Praministan Spain Jose Luis Rodriguez Zapatero
Image caption Praministan Spain Jose Luis Rodriguez Zapatero

Asusun ba da lamuni na IMF, ya yi kira ga kasar Spain da ta yi gagarumin garambawul ga tattalin arzikinta.

Yayin da ake ta kara nuna damuwa a kan bashin kasar, da kuma alamun farfadowar da ba ta da karfi, IMF ya ce lalle ne a yi sauye-sauye game da ma'aikatan kasar, bangaren da ya nuna ba ya aiki sosai.

Sai dai jagoran babbar kungiyar 'yan kwadago ta Spain, Candido Mendez, ya ce ba za su amince da rage yawan ma'aikata ba.

Ya ce, suna matukar adawa da tilasta yin garambawul ta fannin ma'aikata, irin yadda IMF ke bukata, abin da a karshe zai rage yawan ma'aikata a kasar.