'Yan Ghana na gudun hijira zuwa Togo

Shugaban kasar Ghana
Image caption Akwai kalubale a gaban shugaba John Atta Mills, na shawo kan wannan rikicin

Ministan tsaro na kasar Togo, ya ce kimanin 'yan gudun hijira 3,500 ne suka tsallaka zuwa arewacin kasar daga Ghana.

Yakara da cewa suna cikin wadanda rikicin kabilanci dana kan iyaka ya rista da su a yankin Nandom na arewacin kasar.

'Yan gudun hijirar sun fara isa kasar ne a makon da ya gabata, kuma mafiya yawansu mata ne da kanan yara da kuma matasa.

Wakilin BBC a Togo, tace 'yan kasar Ghana na tsallakawa zuwan arewacin Togo, domin gujewa fadan da aka dade ana tafkawa a 'yan kwanakin nan.

Kuma a yanzu an kafa sansani na wucin gadi a yankin Tandjouare dake arewacin Togo.

Bayan ya ziyarci sansanin, Ministan tsaro Kanal Mohammed Atcha Titikpina, ya ce: "munzo ne a madadin gwamnatin Togo domin nuna alhini ga 'yan uwanmu na kasar Ghana.

"Babban abinda yake gabanmu shi ne na samar wa wadannan mutane kayan agaji na gaggawa, da suka hada da abinci da tsaro da matsuguni na waucin gadi".

A tsakanin shekarun 1994 da 1995, rikicin filaye a arewacin Ghana ya rikide zuwa na kabilanci, abinda ya haifar da asarar rayuka kusan 1,000, tare da tarwatsa kimanin wasu karin 150,000.