An mika sunan mataimakin gwamnan Jihar Kaduna

Patrick Yakowa
Image caption Mista Patrick Yakowa, Gwamnan Jihar Kaduna

A jihar kaduna da ke Arewa maso yammacin Najeriya wasu sun fara nuna damuwa a bisa zaben Alh Muktar Ramalan Yero a matsayin wanda bayanai suka nuna cewa shi aka mika sunansa domin na zama mataimakin gwamnan jihar.

A yayin da wasu ke ganin wanda aka bayyana ya cancanta,wasu kuwa na zargin tsohon gwamnan jahar ne da neman yin katsalandan inda ya dage sai an nada wani na hannun daman sa, Alhaji Muktar Ramalan Yero wanda shine kwamishinan kudin jahar a matsayin mataimakin gwamna.

Sai dai kuma gwamnatin Jihar ta musanta haka.

Ammah kuma sanadiyyar dambarwar da ake fama da ita, bayanai sun nuna cewa an `kara mika sunayen wasu mutune 2 a jerin sunayen ga majalisar dokokin jahar domin tantancewa.

A makon daya gabata ne dai aka rantsar da Mista Patrick Ibrahim Yakowa a matsayin sabon gwamnan Jihar Kaduna, bayan da shugaban kasar Najeriya ya nada gwamnan jihar, Arcitect Namadi Sambo a matsayin mataimakin shugaban kasar.