Kariya ta Arewa ta yanke hulda da ta Kudu

Jirgin ruwan Koriyan da aka nitsar

Koriya ta Arewa ta sanar cewa ta katse duka huldarta da Korea ta Kudu.

Wannan mataki dai ya biyo bayan karuwar zaman zullumi ne tsakanin kasashen biyu, sakamakon nitsar da wani jirgin ruwan yakin Koriya ta Kudun a cikin watan Maris da ya gabata.

A 'yan kwanakin nan dai, Korea ta Kudu ta ce za ta haramta wa jiragen ruwan Koriya ta Arewa shiga cikin ruwayenta, sannan kuma za ta kaste kusan duka huldar cinikayya da Korea ta Arewan.

A makon jiya ne dai, Koriya ta Kudu ta wallafa sakamakon wani binciken kasa da kasa, wanda ya dora alhakin nitsar da jirgin ruwanta a kan Korea ta Arewa.

Sai dai Korea ta Arewan ta musanta cewa tana da hannu a al'ammarin.

Yunkurin Diflomasiyya

A yanzu dai yunkurin diplomasiyyar da aka sa a gaba shi ne, yadda yakin cacar bakan da ake yi a yankin Koriyan ba zai rikide ya zama zazzafan rikici ba.

Matsayin da Korea ta Arewa ta bayyana na yanke duk wata alaka da Koriya ta Kudu dai ya biyo bayan wadansu rahotanni masu zaman kansu, wadanda ke bayyana cewa wani makami ne ya nutsar da jirgin ruwan Korea ta Kudu a watan Maris din da ya gabata.

Mutane 46 ne dai suka rasu a cikin jirgin ruwan, kuma Korea ta kudu na zargin ta Arewa da alhakin haka, batun kuma da gwamnatin Pyongyong wato babban birnin Koriya ta Arewan ta musanta.

Korea ta Arewan ta fitar da wata sanarwa ta gidan talabijin din kasar dake gargadin Sojin Koriya ta Kudun.

Sanarwar tace "a kwanakin nan sojin ruwan Korea ta Kudu na shiga cikin ruwanmu. Suna yin abubuwan dake takalarmu ta hanyar ketarowa cikin ruwanmu tun daga ranar 14 ya zuwa ranar 24 ga watan da muke ciki. Wannan tsokana ce da gangan domin taso da wani yaki. Idan har Koriya ta Kudun ta cigaba da ketarowa ta cikin ruwan mu, to Koriya ta Arewa za ta dauki matakin soji domin kare ruwanta."

Yanke Hulda

Tuni dai Koriya ta Kudu ta yanke duk wata alakar tattalin arziki da ta Arewa, kuma tana shirin kai maganar wurin majalisar dinkin duniya.

Amurka dai ta goyi da bayan wannan matakin, sai dai duk iya lokacin da sakatariyar harkokin wajen Amurka wato Hillary Clinton ta shafe a babban birnin Beijin na kasar Sin, bata ji ko da tari da zai kalubalanci Korea ta Arewa ba daga bakin jami'an Sin din ba.

Fatan ta zai kasance Beijing ta shaida wa Pyongyong da kada ta soma rura wutar tashin hankali.

Sai dai kuma mai magana da yawun ma'aikatar wajen kasar Sin Jiang Yu ta yi kira ne ga duka bangarorin biyu da su dauki hakuri.

Tace "ina ganin samun zaman lafiya da daidaito a yankin Koriya da ma Arewa maso gabashin nahiyar Asiya shi ne abinda kowacce kasa a yankin ke so, kuma wannan wani aiki ne na bai daya ga duka kasashen.

"Zamu warware duk wata matsala ta kasashen waje, ko kuma ta yankin bisa ga gaskiya da adalci, akan wanda yayi daidai da wanda ya saba. A wannan yanayin duk wani mataki da wani zai dauka ya kamata ya kasance domin samar da zaman lafiya da daidaito ga kasashen Korean, ba sabanin haka ba.

Babu dai wanda zai fi damuwa da samun zaman lafiya da daidaito a tsakanin takwarorin Korean da ya wuce Sin.