'Yan kasuwa a Nijar sun yi barazanar shiga yajin aiki

Salou Djibo
Image caption Shugaban gwamnatin mulkin sojin NiJar, Salou Djibo

Wasu yan kasuwa a Jamhuriyar Nijar sunyi barazanar dakartar da shigowa da kayayaki da suke safarar su ta tashar jiragen ruwan Cotonou dake jamhuriyar Benin

Yan kasuwar dai sun ce sun dauki wannan matakin ne don maida martani ga wani shiri da hukumomin `kasar ta Benin suka dauka na cewa duk man girkin da zai shigo Nijar daga Cotonou sai an auna shi a wajen jami'an kwastan din `kasar.

Abin da kuma yan kasuwar ta Nijar suka ce ba za su amince da shi ba, saboda a cewarsu, matakin ya sabawa yarjejeniyar da ke tsakanin kasashen 2.

Shuagban kungiyar yan kasuwa ta Nijar Alhaji Samaila Mai Aya ya fada ma BBC cewa , hukomomin Benin sun dau wanan matakin ne ba tare da tuntubar yan kasuwa ta Nijar ba , kuma muddin kasar ta Benin bata canza shawara ta ba, uwar kungiyar zata umurci yan kasuwar su sauya tashar jirgin ruwa a wata kasar.