Akwai damuwa kan ayyukan jin kai a Chadi

An dade ana gwabza fada tsakanin gwamnatin Chadi ta 'yan tawaye

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, tace ayyukan jin kan da majalisar ke gudanarawa a kasashen Chadi da jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ka iya fuskantar matsala.

Mai magana da yawun hukumar ya gayawa BBC cewa yana "takaicin" hukuncin da aka yanke na janye sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya daga kasashen. Sojojin wadanda adadin su yakai 4,375-za su fara janyewa ne a hankali daga karshen bana.

An tura su kasar ne domin bayar da kariya ga dubban daruruwan 'yan kasar ta Chadi da wadanda suka yo gudun hijira daga yankin Darfur na kasar Sudan.

Gwamnatin kasar Chadi ce dai ta nemi Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya janye sojojin.

Zaman dar dar

Image caption Jama'a da dama sun kauracewa gidajen su sakamakon fadace-fadace

"Mun fahimci dalilin daukar matakin, amma muna kokawa game da makomar ayyukan da muke yi a gabashin Chadi," ata bakin mai magana da yawun Hukumar ta UNHCR, Mans Nyberg

" Idan suka fice to dole ne mu rage ayyukan da muke yi".

Mista Nyberg yace ana samun karuwar hare-hare a gabashin Chadi a kullum, inda ake zaman dardar.

Ya kara da cewa sojojin suke samar da tsaro a yankin fiye da jami'an tsaron gwamnatin Chadi.

Akawi kimanin 'yan gudun hijira 260,000 a Chadi, wadanda suka tsallako iyaka daga yankin darfur inda ake fama da rikici.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International, tayi gargadin cewa matakin da majalisar ke shirin dauka ka iya jefa 'yan gudun hijirar cikin La haula.

Kimanin kashi daya bisa uku na sojojin ne za su fara janyewa daga watan Yuli, kafin su janye baki daya awatan Oktoba.

Akwai dai kimanin sojoji 3,300 da kuma jami'an tsaro masu farin kaya 1,075 a Chadi da kuma jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Ita ma kasar Faransa nada sansanin soji biyu a kasar, sai dai ba aikin kiyaye zaman lafiya suke yi ba, duk da cewa a wasu lokutan sukan taimaka wajen kare gwamnati daga hare-haren 'yan tawaye. A farkon bana shugaban Idriss Deby ya bayyana sojojin Majalisar ta Dinkin Duniya da cewar ba su da amfani.

Wannan matakin dai na zuwa ne adan dai lokacin da dangantaka ke kara farfadowa tsakanin Chadi ad Sudan.

Sai dai awatanni ukun da suka gabata, an samu barkewar rikici a gabashin chadi, inda gwamnati tace ta kashe 'yan tawaye 100.