Isra'ila ta kai hare-hare kan Zirin Gaza

Israila ta kaddamar da wasu jerin hare-hare ta sama a kan Zirin Gaza.

Hare-haren sun shafi wani yanki ne kusa da Beit Hanoun a arewa, da kuma wani filin tashi da saukar jiragen sama da ba a amfani da shi a kudu.

An bayyana cewa mutane da dama sun samu raunuka sakamakon hare-haren.

Wani mai magana da yawun kasar ta Israila ya ce hare-haren martani ne ga rokokin da aka harba cikin Israilan daga yankin a ranar Talata.