Kamfanin mai na BP ya sake dabara

Wata agwagwar ruwa wadda mai ya lullube
Image caption Wata agwagwar ruwa lullube da mai tana neman mafaka a jikin wani jirgin ruwa a inda man ya kwarara

Katafaren kamfanin man kasar birtaniya, wato BP, ya fara jarraba wata dabarar toshe rijiyar man da ke kwarara a Tekun Mexico.

Ba a dai taba jarraba wannan dabara ta baya-bayan nan da kamfanin na BP ke yunkurin amfani da ita a karkashin teku ba — dabarar ta kunshi cusa tabo da siminti cikin bututun man da ya huje.

Sai dai jam'ian kamfanin sun ce akwai yiwuwar dabarar ba za ta yi nasara ba; idan kuma dabarar ba ta yi nasara ba, to kwararar man ka iya tsananta.

Akalla lita miliyan ashirin da bakwai na danyen man fetur ne ta gurbata wani yanki mai fadin mil sittin da biyar na gabar tekun Louisiana ya zuwa yanzu, inda man ya lalata muhalli, ya kuma hallaka tsuntsaye da dabbobin ruwa da dama.

Wata kyamarar karkashin ruwan na watsa hotunan bidiyo a wurin da man ke kwarara, al'amarin da ke ba Amurkawa damar kallon irin barnar da annobar ke yi kai tsaye.

Daga gwamnatin Obama har kamfanin BP na shan kakkausar suka game da gazawar da suka yi ta kawo karshen kwararar man.

Ranar Juma'a ne dai ake sa ran shugaban na Amurka da kanshi zai kai ziyara yankin; to amma irin tarbar da mazauna Jihar ta Louisiana za su yi masa ta dogara ne a kan ci gaban da za a samu a sa'o'i ashirin da hudu masu zuwa.