Shugaban Nijar ya ziyarci Najeriya

A yau ne shugaban gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar, Janar Salou Djibo, ya kai ziyara fadar gwamnatin Najeriya.

Wannan dai ita ce ziyararsa ta farko zuwa waje tun lokacin da ya karbi ragamar mulkin kasar ta Nijar a watan Fabrairun da ya wuce, bayan sojoji sun hambare Shugaba Tandja Mammadou. An dai yi tsammanin cewa shugaban na Nijar zai tattauna ne da mahukuntan Najeriya a kan al'amuran da suka shafi siyasa a kasar Nijar, da kuma kawancen da ke tsakanin kasashen biyu.

To amma sai aka bayyana cewa ziyarar ta'aziyya ce dangane da rasuwar tsohon shugaban Najeriya, marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar'aduwa.