Kamfanin BP ya rage yoyon mai a gabar tekun Mexico

malalar mai a yankin tekun Mexico
Image caption Ko tabo da siminti za su taimakawa BP cimma burin sa?

Rohatanni na nuna cewa Kamfanin mai na BP mallakar Burtaniya, ya rage malalar mai da gas wanda ke yoyo a gabar tekun Mexico.

Wani kwamandan rudunar tsaro na ruwan Amurka Admiral Thad Allen, ya ce sabuwar dabarar da Kamfanin ya bullo da ita ta fara aiki, a yayayin da malalar man ya ragu.

Jami'in ya ce wannan ne mataki na farko, kuma ba za a iya tantancewa ko sabuwar dabarar za ta magance matsalar ba.

Hakan na zuwa ne adai dai lokacin shugaba Obama ya kori jami'in da ke kula da lafiyar rijiyoyin mai na kasar, Elizabeth Birnbaum.

Kuma nan gaba kadan ake saran zai bada sanarwar dakatar ayyukan hako mai a cikin teku har na tsawon watanni shida.

Abinda ke nufin za a soke ayyukan kwangilar da ake gudanarwa a gabar tekun Mexico dana Virginia da Alaska.

Masana muhalli

Harwa yau dai masana sun ce malalar man wanda ya auku a watan Afrilu, ya yi matukar illa fiye da yadda aka kimanta da farko.

Wasu 'yan majalisun dokokin Amurka guda biyu sun bayyana cewa wasu takardu sun nuna cewa an samu gargadi kafin wadannan fashe-fashe, amma sai aka dauki mataki a makare.

Maikatan kamfanin goma sha daya ne suka rasa rayukansu sakamakon fashewar bututun man a watan Afrailu.

Kamfanin ya yi asarar miliyoyin gangunan mai wanda kuma masana sukace zai gurbata muhalli.