Kungiyar Amnesty ta soki manyan kasashe

Sakataren kungiyar Amnesty International
Image caption Sakataren kungiyar Amnesty International, Claudio Cordone ya ce wadansu kasashen suna ganin sun fi karfin doka

Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta yi suka a kan abin da ta kira shigar da siyasa cikin tsarin tabbatar da adalci da shari'a na duniya.

A wani rahoton da ta saba fitarwa shekara-shekara, kungiyar ta kuma zargi kasashen duniya da laifin daukar siyasa da muhimmanci fiye da tabbatar da adalci.

Rahoton kungiyar Amnesty International din na baya-bayan nan dai wani kundi ne laifuffukan keta hakkin bil-Adama da ta ce an aikata a fadin duniya.

Rahoton ya ambato yadda aka ganawa mutane ukuba a kasashe dari da goma sha daya, da shari'ar da aka yiwa wasu ba bisa adalci ba a kasashe hamsin da biyar da kuma tauye 'yanci fadin albarkacin baki a kasashe casa’in da shida.

Rahoton ya kuma zargi gwamnatocin kasashe masu karfin fada a ji da yin kafar ungulu ga yunkurin tabbatar da adalci a duniya.

Babban Sakataren riko na kungiyar, Claudio Cordone, ya ce wasu kasashen ma suna nuna cewa sun fi karfin doka.

“Saboda rashin rattaba hannu a kan yarjejeniyar da ta kafa kotun hukunta mayan lafuffuka ta kasa-da-kasa, kasashe irin su Amurka da China da Rasha da Indiya suna nuna cewa sun fi karfin doka”, inji Mista Cordone.

Rahoton ya kuma yi suka a kan kasashen Tarayyar Afirka saboda gazawar da suka yi ta aiwatar da umurnin kotun kasa-da-kasa na kama Shugaba Omar al-Bashir na Sudan.

Sai dai ya bayyana umurnin, wanda shi ne irinsa na farko, da cewa gagarumin ci gaba ne ga yunkurin tabbatar da adalci a duniya.