A samu rikicin makiyaya da manoma a jihar Neja

Taswirar Najeriya
Image caption 'Yan sanda sun musanta rikicin ya kashe mutane arba'in

Rohotanni daga jihar Neja a arewajin Najeriya na cewa yanzu haka hankali ya fara kwantawa a wasu kauyuka da ke cikin karamar hukumar Lapai ta jihar, bayan wani tashin hankali da ya auku.

Rikicin ya auku ne tsakanin Fulani makiyaya da mazauna kauyukan.

Rohotanni na nuna cewa rikicin ya samo asali ne a sakamakon zargin da mazauna kauyukan suka yi cewa Fulanin na kora dabbobinsu cikin kan wata makabarta.

Rikicin dai ya janyo asarar rayuka da dukiya mai dimbin yawa, ko da yake hukumonin tsaro na musanta cewa an samu asarar rayukan.