An sake rantsar da shugaba al-Bashir na Sudan

Shugaba el-Bashir na Sudan
Image caption Kotun duniya ta dade tana farautar shugaba el-Bashir

An sake ranstar da shugaban Sudan Umar al-Bashir akan karagar mulki, bayan ya lashe zaben kasar da aka gudanar a watan da ya gabata, wanda ke cike da rudani.

Kotun kasa da kasa mai hukunta laifukan yaki na neman shugaba Bashir, kan zargin aika laifukan yaki ayankin Darfur.

Da dama daga cikin shugabannin kasashen duniya basu halarci bikin ba, amma akalla anga shugabannin Afriak guda biyar.

Majailisar Dinkin Duniya tace za ta tura shugabannin rundunar kiyaye zaman lafiya biyu da ke kasar zuwa wajen bikin rantsuwar.

Da yake ranstuwar kama aiki, shugaban ya yi jawabi ga majalisar dokokin kasar har na tsawon mintuna 30.

Shugabannin kasashen Ethiopia da Chadi da Malawi da Mauritania da Djibouti duk sun halacci bikin. Sai dai kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch, tace shugabannin da ke son tabbatar da adalci a yankin Darfur, bai kamata su halacci bikin.

Amma wani babban jami'i a jam'iyya mai mulki yayi allawadai da kalaman kungiyar.

Image caption Jama'a sun fito sosai a lokacin zaben da ya maida shugaba Bashir kan mulki

Watanni masu mahimmanci

A rahotanta na shekara-shekara,kungiyar Amnesty International, tace har yanzu ana ci gaba da cin zarafin jama'a, duk da cewa fadan da ake yi bai kai na baya kamari ba.

A wata hira da BBC, wani jami'in kungiyar wanda ya kware kan nahiyar Afrika, ya karyata kalaman cewa bikin rantsuwar da aka yi, ya nuna cewa kotun ta duniya ta gaza.

"Babu shakka zai kawo cikas da shari'a, amma bai nuna gazawar kungiyar ba".

Wakilin BBC James Copnall a birnin Khartoum, yace hakan ka iya karfafawa shugaba Bashir gwuiwa, amma sai dai har yanzu bashi da farin jini a idon wasu.

Watanni masu zuwa nada mahimmanci sosai ga shuagaba Bashir.

A watan Janairu, 'yan kudancin kasar za su kada kuri'a domin neman cin gashin kai, a wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiyar da ta kawo karshen yakin da aka dade ana gwabzawa. Shugaban dai ya yi kira da ahada kai, amma zai yi wuya kudancin basu balle ba, idan dai har an gudanar da zaben cikin adalci.