ECOWAS na cika shekaru 35 da kafuwa

Taswirar Afirka ta Yamma
Image caption Kasashe goma sha biyar ne a kungiyar ECOWAS/CEDEAO

A yau ne Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS ko CEDEAO) ke fara bukuwan cika shekaru talatin da biyar da kafuwa.

An dai shirya za a yi bukukuwa da dama a hedkwatar kungiyar da ke babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

An kafa kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO ne don wanzar da kasuwanci a tsakanin kasashe goma sha biyar din da ke Yammacin Afirka.

Sai dai yayin da mahukunta a kasashen Yammacin Afirkan ke ganin cewa hukumar ta taka rawar gani a shekaru talatin da biyar din da suka gabata, wadansu na ganin har yanzu akwai jan aiki a gaba, saboda dimbin kalubalen da ke gaban kungiyar wajen wanzar da kasuwanci da ci gaban tattalin arziki a yankin.