Hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya ta yi gargadi game da karancin abinci

Wata mata na shikar hatsi
Image caption Wata mata na shikar hatsi

Hukumar bayar da taimakon gaggawa ta Nigeria, watau NEMA, ta yi gargadin cewar mutane miliyan goma sha biyu a arewacin kasar suna fuskantar karancin abinci.

Darakta Janar na Hukumar, Mohammed Audu Bida, ya ce wasu shanu kamar dari ukku sun mutu a Jihar Sokoto, sannan kuma wasu cuttutuka kamar kwalara da zazzabin cizon sauro za su kara yin kamari a yankin.

Hukumar ta NEMA ta ce karancin ruwan sama da yankin ke fuskanta ne zai iya haddasa matsalar ta karancin abinci.

Hukumar ta ce, jihohi goma sha daya ne a arewacin Nigeria za su iya fuskantar matsalar.

Ma'aiaktan agaji a Niger da ke makwabtaka da Nigeria sun ce mutane kamar miliyan bakwai ne a can ma, watau kusan rabin al'ummar kasar suke fuskantar karancin abinci.