Yiwuwar karancin abinci a Najeriya

Karancin abinci a Najeriya
Image caption Ana danganta karancin abinci da rashin kyawun damuna

A Najeriya, rahotanni daga hukumar bada taimakon gaggawa ta kasar NEMA, na cewa Arewacin kasar na fuskantar barazanar yunwa da karacin abinci.

Ana kallon Arewacin Najeriya a matsayin yankin dake samar da abinci a kasar, saboda yawancin kayan abinci na fitowa ne daga wannan yanki.

A cewar hukumar ta NEMA karancin abincin ka iya faruwa ne sakamakon karancin ruwan sama da yankin ya fuskanta.

A cewar hukumar, jihohi goma sha daya ne a arewacin kasar za su fuskanci matsalar.

Wakilin BBC Muhammad Abba, yace wannan ka iya kasancewa wata hanya da kasar za ta farga daga irin matsalar da wannan hasashen idan ya tabbata zai iya haifarwa ga Najeriya.

Matsalar yunwa

A halin yanzu tuni aka bayyana kasashen Chadi da Niger wadanda ke makwabta da Najeriyar, a matsayin wadanda ke fama da matsalar yunwa.

Jihohinda ka iya fuskantar FARI kamar yadda hukumar ta sanya a shafinta na intanet, sun hada da Sokoto da Katsina da zamfara.

Dama jihohin kebbi da Jigawa da Kano da Borno da Yobe da Gombe da Bauchi da Adamawa.

Masana

Dakta Nasiri Ibrahim, wani masani a kan tsirrai dake Jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato, ya shaidawa wakilin mu Haruna Shehu Tangaza cewa:

Image caption Wasu mata na noma a nahiyar Afrika

"Wadatar abinci na ta'allaka ne da ruwan saman da aka samu, kuma yawan ruwan ba shi ne abin la'akari ba, amma yanayin da zo shi ne mai mahimmanci".

"Baya ga wannan kuma akwai matsalar sauyin yanayi wacce ke tasiri kan makomar aikin gona," a cewar masanin.

Haka kuma akwai bukatar la'akari da irin da ya kamata manoma suyiamfani da shi, da kuma lokacin da ya kamata ayi shukar kanta.

Malamin yace ya kamata gwamnati tayi tanadi a irin wannan yanayi, sannan ta nemi ra'ayin masana idan irin wannan ta faru.

Hukumar ta NEMA tace ya zama tilas ta bada wannan gargadi, domin a dauki matakan shawo kan lamarin ta hanyar fadakar da manoma domin su yi tanadi don kaucewa munin lamarin.

Hakazalika sanarwar da hukumar ta fitar zai taimakawa gwamnatocin jihohin da abin zai fi shafa, da ma gwamnatin tarayya, su fara binciken hanyoyin da za su bi su tunkari matsalar.

Hanyoyin tunkarar matsalar kuwa, sun hada da samarwa manoma IRI wanda karancin ruwan sama ba zai hana shi tsirowa ba.

Da samar da takin zamani ga kananan manoma cikin farashi mai rahusa ta yadda ba za su wahala ba wurin inganta aikin nomansu.

Wannan ka iya taimakawa wurin rage radadin matsalar ta FARI. Masu iya magana dai kan ce Idan kunne ya ji to jiki ya tsira.