Kasashe na son hana yaduwar nukiliya

Pirayi Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu
Image caption An yi suka akan yadda aka ware kasar Israila daga taron

Wani babban taro kan yadda za a magance yaduwar makaman nukiliya ya amince da a hada kai wajen tabbatar da ganin an kawar da dukkanin makaman kare dangi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Shawarar tana da muhimmanci wajen samun nasarar taron da aka shafe wata daya ana gudanarwa, inda kasashen suka sanyawa yarjejeniyar hana bunkasar makaman nukiliyar hannu.

Wannan shi ne babban yunkurin kasashen duniya wajen kaucewa yaduwar makaman nukiyar, don haka ne ma kasar Amurka ta goyi bayan shirin, sai dai ta yi suka ga yadda aka ware kasar Israila.

Yankin Gabas ta Tsakiya dai yana fama da rikice-rikice wadanda ake ganin rage yaduwar makaman kare-dangin zai magance su.