Wani babban minista yayi murabus a Britaniya

Minista David Laws
Image caption Minista David Laws

Wani babban minista a sabuwar gwamnatin gambiza ta Birtaniya, David Laws, ya yi murabus bayan an gano cewa ya karbi dubban daloli daga baitulmali, don biyan kudin haya ga abokin luwadinsa na dogon lokaci.

Dokokin Birtaniya dai sun haramta wa 'yan majalisar dokokin kasar yin hayar gida daga abokan zamansu.

A wani taron manema labarai, Mr Laws, wanda dan jam'iyyar Liberal Democrat ne, ya ce ba zai iya cigaba da aikinsa ba, na kula da batun tsuke bakin aljihun gwamnati, yayinda ya ke cikin wannan hali.

Tun farko dai Mr Laws ya ce bai bayyana wa majalisar dokoki halin da yake ciki ba, saboda ba ya son jama'a su san cewa shi dan luwadi ne.