Sabon nau'in cutar shan inna a jahar Borno

Samfarin rigakafin polio
Image caption Samfarin rigakafin polio

Jami'an kungiyar lafiya ta duniya a jahar Borno sun ce an gano wani sabon nau'in kwayar cutar shan inna da ake kira type 2, a unguwar Fulatari da ke Maiduguri.

A yau jami'an kiwon lafiya suka bazu cikin unguwar ta Fulatari dama sauran unguwannin dake kewaye da ita, domin sake yiwa yara rigakafin polion.

Cutar ta bulla ne yayin da ake shirin gudanar da wani gangami na ci gaba da yaki da ita, a jihohin Najeriya da suka fi fama da polion.

Najeriya na daga cikin jerin kasashen da har yanzu aka kasa shawo kan cutar shan innar, saboda kyamar da wasu ke nuna wa rigakafin ta, bisa dalilai irin na addini.