Amirka ta damu akan tsiyayar mai a tekun Mexico

Tsiyayar mai a Tekun Mexico
Image caption Tsiyayar mai a Tekun Mexico

Kwana daya bayan da kamfanin mai na BP ya gaza toshe bututun da ke tsiyayar da mai a tekun Mexico, fadar White House ta nuna rashin kyakyawan fata dangane da irin abubuwan da zasu biyo baya.

A wata hira da gidan talabijin na NBC, mai ba shugaba Obama shawara ta fuskar makamashi, Carol Browner, ta ce mai yiwuwa man ya cigaba da tsiyaya har zuwa cikin watan Agusta.

Ta ce watakila lamarin ya kasance bala'i mafi muni da aka taba fuskanta a Amirkan.

Yanzu kamfanin BP zai yi amfani da wasu na'urori da ake sarrafawa daga nesa ne don yanka bututun.

Bayan haka za a dasa wata na'ura a jikin bututun, ta yadda man zai rika tsiyaya zuwa wani jirgin ruwa.