Mutane 30 sun hallaka a hatsarin mota a Kamaru

Taswirar Kamaru
Image caption Taswirar Kamaru

Akalla mutane 30 sun rasa rayukansu, a wani hatsarin mota da ya faru a Kamaru.

Rahotanni sun ce motar safa ce ta kubce wa direbanta, ta yi ta jujjuyawa, kamin daga karshe ta fada cikin wani rami dake kan hanya.

Hatsarin ya auku ne a wani yanki mai nisan wajejen kilomita 135 a arewacin Yaounde, babban birnin kasar.

Jami'an tsaro masu bada hannu sun ce hatsarin ya yi munin gaske, ta yadda har motar ta daare gida biyu.

Motar safar tana kan hanyar zuwa birnin Yaounde ne, bayan ta taso daga garin Bafoussam dake yammacin kasar ta Kamaru.