Gurbatacciyar iska ta lahanta mutane a Kaduna

Rahotanni da jihar Kaduna a Najeriya sun ce daruruwan mutane sun jikkata bayan da suka shaki wata gurbatacciyar iska dake fitowa daga wasu kayayyakin masana'antu.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kaduna, Alhaji Aliyu Saleh Ramin Kura, ya shaidawa BBC cewa an kai mutanen da suka jikkata asibiti, inda daga bisani aka sallami wasu daga cikinsu, bayan da aka tabbatar da lafiyar su. Wadanda suka shaki gurbatacciyar iskar na suma ne.

Ya kara da cewa hukumarsa da hadin gwiwar jami'an tsaro, za su dauki matakin hukunta mutumin da ake zargi da kawo kayan da ke kunshe da gurbatacciyar iskar

Ya ce gwamnatin jihar, da hukumarsa, da ma sarakunan gargajiya, suna wayarwa mutane kai dangane da illar irin wadannan sinadarai.