Wani Bishop ya yi murabus bayan aikata abin kunya a Najeriya

bishop-bishop din cocin Katolika

Fadar Vatican ta amince da murabus din da wani Fadan coci dan asalin jamhuriyar Ireland ya yi, bayan an zarge shi da yin lalata da wata karamar yarinya a yankin Naija Delta.

Richard Burke, wanda shi ne archibishop na birnin Benin, ya aminsa yin tarayya da yarinyar, amma ya musanta cewa karamar yarinya ce a lokacin da suka fara hulda.

"Dalilin yin murabus dina shi ne, na karya alkawarin rantsuwar da na dauka na kama kai daga duk wani jima'i da mata" in ji bishop din, a wata sanarwar da aka wallafa a wata jaridar Katolika ta jamhuriyar Ireland.

Archibishop din ya sauka daga mukaminsa ne bayan zargin da aka yi a shekarar da ta gabata.

Dolores Atwood, ta yi zargin cewa, Archibishop Burke ya ci zarafinta ta hanyar yin lalata da ita a lokacin da yake jagorancin cocin katolika na Warri dake yankin Naija Delta.

Sai dai bishop din ya ce, ya fara hulda da ita ne a shekarar 1989, a lokacin tana 'yar shekara 21 shi kuwa yana da shekaru 40.

Archibishop Burke ya kuma nemi gafarar Ms Atwood da mabiyansa na Warri da Benin.

Fadar Vatican ta ce ta amince da murabus din, ta kuma nada wani kwamiti da zai duba matsalar cin zarafin yara kanana da fada-fadan resehen cocin na jamhuriyar Ireland suka yi.