Shugaban Jamus yayi murabus

 Shugaba Koehler mai murabus
Image caption Shugaba Koehler mai murabus

Shugaban kasar Jamus, Horst Koehler, ya yi murabus bayan shan suka kan kalamin da yayi game da yin amfani da dakarun tsaron Jamus a kasashen waje.

Bayan da ya koma gida daga Afghanistan, ya ce yakin da Jamus ke yi a waje zai iya zama wajibi domin kiyaye bukatunta na cinikayya.

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce ta yi mamaki game da murabus dinsa, sannan ta yi kokarin ya sauya ra'ayinsa.

An dai dauki kalamun nasa da nufin tura dakarun da Jamus ta yi zuwa Afghanistan, abinda kuma ya janyo cece -kuce, to amma daga bisani Ofishinsa ya ce batun fashi a tekun Somalia ne ke cikin ransa.