PDP ta dage dakatarwar da ta yiwa wasu 'ya'yanta

 Shugaba Goodluck na Najeriya
Image caption Shugaba Goodluck na Najeiya

Jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta janye korar da ta yiwa wasu mambobinta sha tara da ta zarga da nuna rashin da'a ga shugabanci da dokokin jam'iyyar ta hanyar kafa wata kungiya mai suna PDP Reform Forum.

Kungiyar ta PDP Reform Forum dai tana neman a kawo sauyi ne a yadda ake tafiyar da jam'iyyar mai ikirarin kasancewa mafi girma a nahiyar Afurka.

Wasu 'yan jam'iyyar PDP dai sun jima suna kokawa akan yadda ake tafiyar da jam'iyyar inda wasu ke zargin masu rike da mulki da kwace tafiyar da jam'iyyar ta bayan fage.