Kasashen duniya sun yi Allah wadai da Isra'ila

Jirgin ruwan
Image caption Jirgin ruwan da Isra'ila ta kama, sannan ta kashe wasu 'yan fafutuka

Bayan wata tattaunawa da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar, ya yi kira da a gudanar da bincike kan harin da dakarun Isra'ila suka kai kan jiragen ruwan dake dauke da kayan agaji zuwa Gaza a ranar Litinin.

Sanarwar da kwamitin sulhun ya amince da ita, ta ce binciken zai kasance a kan lokaci, a bayyane ba tare da nuna son kai ba, kuma cikin gaskiya.

Har yanzu dai babu tabbaci dangane da makomar kayan agajinda jiragen ruwan ke dauke da su, a wani yunkuri na kawo karshen toshe iyakokin Gaza da Israela ke yi na tsawon shekaru ukku.

Jiragen ruwan guda shidda da Israela ta kwace, ta sauya akalarsu zuwa gabar tekun Ashdod.

Martani

Tuni dai klasashen duniya suka ti kakkausar suka kan matakin da Isra'ilan ta dauka.

Kasar Turkiyya tayi matukar Allah wadai da Isra'ila a wani taron gaggawa da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira dangane da harin da sojin suka kai.

A kalla masu gwagwarmayar kwato yancin Palasdinawa guda tara ne suka rasu, ciki har da yan kasar ta Turkiyya, a lokacin da dakarun Israela suka aukawa jirgin ruwan a tekun kasa da kasa.

Ministan kula da harkokin wajen Turkiyya Ahmet Davutoglu yace a bayyane take cewa an aikata laifi, a tekun kasa da kasa.

"Babu wata kasar dake da ikon dakatar da wani jirgin ruwa, domin yi masa tambayoyi ko ma kaiwa jirgin hari. Yan fashi a teku ne kawai ke yin haka.

Sai dai Ministan tsaron Israela Ehud Barak, ya ce yana fata kasashen duniya su fahimci irin barazanar da kasarsa ke fuskanta a ko wanne lokaci daga Hamas a Gaza.

To amma wakilin hukumomin Palasdinawa a birnin London Manuel Hassassian,, ya shaidawa BBC cewa Isra'ila kamar yadda yace, ba za ta iya ci gaba da kuntatawa Palasdinawa tana fakewa da sunan tsaro ba.

"Kamata yayi kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya dauki wani kwakkwaran mataki kan Israela, kuma a gani na ya kamata a gudanar da bincike sosai dangane da abinda ya auku, sannan a hukunta wadannan miyagun mutanen nan masu aikata laifukan yaki".

"Zummar a zauna lafiya"

Ita ma Kungiyar hadin kan larabawa, wadda ke gab da gudanar da taron gaggawa, ta ce abinda Isra'ila tayi ya nuna karara cewa, ba ta da zummar a zauna lafiya.

Jiragen ruwa shidda ne dai Israela ta kwace, ta sauya akalarsu zuwa gabar tekun Ashdod.

Wasu mutanen dake jiragen kamar tsohon jamiin diflomasiyya na Amurka, an tura su kasashensu, yayinda Isra'ila ta tsare wasu.

Har yanzu dai babu tabbaci dangane da makomar kayan agajin da jiragen ruwan ke dauke da su, a wani yunkuri na kawo karshen toshe iyakokin Gaza da Israela ke yi na tsawon shekaru ukku.

Isra'ila ta ce za ta kai kayan zuwa Gaza ta kasa, kuma ba za ta hada da duk wasu kayanda ta haramta ba.