'Yan Nijar kan hukuncin kisa a Libya.

Wani gidan kaso a Libya
Image caption Wani gidan kaso a Libya .

Wasu 'Yan Nijar dake zaune a gidajen kaso a kasar Libya sun koka kan matsanancin halin da suke ciki, inda suke zargin jami'an tsaron kasar na kama su, ana kuma yanke musu hukuncin da ya kama daga na dauri zuwa na kisa, a galibin lokutta, ba da laifinsu ba.

Kwanaki biyu da suka wuce ne aka bindige wasu 'yan Nijar din su uku bayan da suka shafe sama da shekaru takwas suna jiran a zartar masu da hukuncin na kisa, bisa laifin aikata kisan kai, zargin da su kuma suke ta musantawa.

Cikin wata hira da Sashen Hausa na BBC ya yi da daya daga ciki wadanda ke jira a zartar masu da hukuncin kisan, yayi zargin cewa an rika azabtar ad su ne , suka rika amsa laifukan da ba su aikata ba.

Ofishin jakadancin Nijar a Libya dai ya ce yana iya kokarinsa wajen ganin an saukaka wa fursunonin halin da suke ciki.