Majalisar dattawa ta saurari bahasin jama'a.

Majalisar dokokin Nijeriya
Image caption Majalisar dokokin Nijeriya

A Najeriya, yau ne majalisar dattawan kasar ta fara wani zaman sauraron ra`ayoyin jama`a dangane da gyaran-fuskar da take yi wa kundin tsarin mulkin kasar.

Wannan dai shi ne karo na biyu da majalisar dattawan ke shirya irin wannan taron.

A baya dai majalisar dattawan da kuma majalisar wakilan kasar duk sun saurari ra`ayoyin jama`a.

Hakan ne kuma ya ba su damar yin wasu gyare-gyare ga kundin tsarin mulkin kasar, inda majalisar dattawan ta bayyana cewa zata tura matsayinta zuwa majalisun dokokin jihohi kafin ta kammala aikin kwaskwarimar, amma sai aka wayi gari da wani sabon zama na sauraron ra`ayin jama`a.