Wata ta kashe mijinta saboda kishiya

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Rahotanni daga jihar Borno a Arewacin Najeriya, na cewa wata mata ta hallaka mijinta har lahira, bayanda ta zuba masa guba a kunu a bisa dalilin yi mata kishiya.

A yanzu rundunar 'yan sanda ta jihar ta Borno, tace tana ci gaba da gudanar da bincike game da wannan mata da ake zargi.

Al'amarin dai ya faru ne a Unguwar Mafoni cikin garin Maiduguri lokacin da ake cikin hidimar bikin marigayin Malam Zarma Musa kafin ya taras da ajalin nasa bayan da aka kaishi asibiti.

Bayanai sun nuna cewa matar ta dade tana sa'insa da mijin nata, tun lokacin da ya daura aniyar kawo mata abokiyar zama.

Rundunar Yan sandan ta bayyana cewar a ranar Laraba ne ake sa ran fitar da sakamakon binciken likitocinda suka duba marigayin wanda zai basu damar daukar matakan da suka dace kan wannan mata da ake zargi da aikata kisan kai.

Kakakin rundunar 'yan sandan ASP Isa Azare, yace matar na hannun rundunar 'yan sandan, wadanda ake saran bayan kammala bincike za su gabatar da ita a gaban Kuliya.