An samu farkar Ibori da laifin halatta kudin haram

Mutum mutumin kotu
Image caption Koliya manta sabo

Wasu masu taya alkali yanke hukunci a wata kotu da ke London, a yau sun samu wata mace da ake zargin farkar tsohon gwamnan Jihar Delta ce, James Ibori da laifin kokarin halatta kudaden haram.

Kotun ta samu Miss Uduamaka Okoronkwo da laifi a tuhume tuhume ukku da aka gabatar a kanta na kokarin halatta kudaden haram.

Kotun ta tsaida ranar litinin bakwai ga wannan watan a matsayin ranar da za ta yanke hukunci a kan Miss Uduamaka Okoronko da kuma 'yar-uwar tsohon gwamnan wato Christine Ibori, wadda ita ma a jiya kotun ta same ta da laifi na kokarin halatta sama da dala miliyan dari.