Isra'ila ta fara masu fafatuka data kama

Daya daga cikin jiragen ruwan da Isra'ila ta kama
Image caption Daya daga cikin jiragen ruwan da Isra'ila ta kama

Isra'ila ta sako fiye 'yan kasashen waje 120 da ta kama bayan da sojojin ta suka afkawa jiragen ruwan dake kokarin keta datsewar da ta yiwa Gaza. An dauki masu fafukar zuwa Jordan. Daruruwan da suka rage, yawancin su 'yan Turkiyya, za a maida su gida nan gaba kadan.

Akalla masu fafutuka tara ne suka rasu, yayinda sojojin kundun bala na Isra'ila suka mamaye jiragen ruwa shida a ranar Litinin.

Kafofin yada labarai a Isra'ila sun bada rahotannin cewa an umarci iyalan jami'an diplomasiyyar kasar da ke Turkiyya da su fice daga kasar.

Turkiyya, wacce na daga cikin kawayen Isra'ila, ta kasance kan gaba wajen Allah wadai da harin da Isra'ilan takai.

Shugaba Obama ya kira takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, inda ya bayyana alhininsa abisa 'yan Turkiyyar da suka rasa rayukansu.

Sakin fursunoni

Kimanin magoya bayan Palatsinawa 120 ne suka isa Jordan ta kan iyaka a ranar Laraba da safe.

Yawancin su sun fito ne daga kasashen Musulmi da basu da huldar jakadanci da Isra'ila, kamar su Malaysia da Indonesia da Bahrain da Kuwait da kuma Pakistan.

Wakilin BBC akan iyakar Isra'ila da Jordan Dale Gavlak, yace jama'a sun taru domin yi musu maraba, inda aka yi ta ife-ife tare da jinjina musu.

An kuma sako wasu masu fafutukar 200 'yan kasar Turkiyya, wadanda ake saran mika su zuwa kasar ta Turkiyya.

A kwai kimanin mutane 30-ciki harda 'yan Burtaniya, dake hannun mahukuntan Isra'ila.

Isra'ila dai tace za ta kammala sakin 'yan fafutukar nan da ranar Alhamis.