Isra'ila ta kare harin da ta kai

 Firayim Minista Benjamin Netanyahu
Image caption Firayim Minista Benjamin Netanyahu

Firayim ministan Isra'ila Binyamin Natenyahu ya kare harin da dakarun Isra'ila suka kai kan jerin gwanon jiragen ruwan kai agaji da suka yi kokarin karya datsewar da Isra'ila ta yi wa Gaza.

A wani jawabi da aka yada a kasar, Mr Netanyahu ya zargi masu sukar kasarsa daga waje da munafinci, ya kuma ce Isra'ila za ta ci gaba da toshe iyakokin zirin Gaza.

Wasu Yan kasar ta Isra'ila sun zargi gwamnatin da tafka kuskure.

Tun farko dai majalisar kasar Turkiya ta amince da wani kudiri wanda ya bukaci gwamnatin Turkiyyar da ta sake duba alakar ta da Isra'ila ta fannin soja da kuma tattalin arziki.Haka nan kuma ta bukaci da a gudanar da bincike da kuma batun biyan diyya kan yan kasarta da aka kashe.