Turkiyya na zama na musamman don duba alakarta da Isra'ila

Frime ministan Turkiyya Tayyib Erdorgan
Image caption 'yan Turkiyya shida ne suka mutu lokacin da sojin Isra'ila suka afkawa jerin gwanon jiragen ruwan masu fafatuka.

Majalisar ministocin Turkiyya na wani zama na musamman da manyan jami'an tsaron kasar domin tattaunawa kan dangantakarta da kasar Isra'ila, bayan da sojin kundumbalar Isra'ilar sun afkawa wasu jiragen ruwan dake kokarin keta datsewar da Isra'ila ta yi wa zirin Gaza a ranar litinin da ya gabata.

A halin da ake ciki dai Isra'ila ta sako dukkan 'yan kasashen wajen da ta tsare a gidan kaso, ciki har da 'yan Birtaniya arba'in bayan farmakin da yayi sanadiyar mutuwar mutane goma, cikin masu fafutukar nemawa al'umar Gaza walwala daga datsewar da Isra'ila ta yi masu.

Wani jirgin ruwan na masu fafutukar nemarwa Gaza 'Yanci na kan hanyarsa na ketare tekun mediterranean dauke da masu fafutuka goma sha daya, wadanda suka bayyana cewa suna kokarin dakatar da tokarar da Israela tayi wa Palasdinu.

Mai Magana da yawun gwamnatin Isra'ila Mark Regev ya bayyana cewa ba za'a iya hana tokarar da suke yiwa Gazan ba.