Jana'izar masu fafutukar da sojojin Isra'ila su ka kashe

Jana'izar masu fafutuka
Image caption Yadda aka yiwa masu fafutuka sallah a Turkiyya

An yi jana'izar mutane tara a Turkiyya da sojojin Isra'ila suka kashe bayan da suka kai hari ga wasu jiragen ruwa da za su kai agaji Zirin Gaza.

An kai akwatunan gawar nade a tutocin Turkiyya da Palatsinu wani masalllaci dake birnin Istanbul.

Jama'a sun taru a wani masallaci domin sallatar mutane taran da suka rasu.

Shugaban da ya jagoranci jirgin dake dauke da masu fafutukar zuwa Gaza Bulent Yildirim ya bayyana cewa har yanzu ba'a san inda sauran wadansu 'yan fafutukar suke ba.

Wasu Jiragen Turkiya ne suka kai gawawwakin birnin Istanbul tare da daruruwan masu fafutukan da Isra'ila ta saki bayan sun tsare sun tun a ranar Litinin.

Jama'a da dama ne su ka yi tururuwa domin yi musu maraba, daga cikinsu harma da mataimakin Firayim Ministan Turkiya Bulent Arinc.

A ranar Laraba ne, Firayim ministan Isra'ila Binyamin Natenyahu ya kare harin da dakarun Isra'ila suka kai kan jerin gwanon jiragen ruwan da suka yi kokarin karya datsewar da Isra'ila ta yi wa Zirin Gaza.

Amma wasu 'Yan kasar ta Isra'ila sun zargi gwamnatin da tafka kuskure.

Tun farko dai majalisar kasar Turkiya ta amince da wani kudiri wanda ya bukaci gwamnatin Turkiyyar da ta sake duba alakar ta da Isra'ila ta fannin soja da kuma tattalin arziki.

Haka nan kuma ta bukaci da a gudanar da bincike da kuma batun biyan diyya kan 'yan kasarta da aka kashe.

Korafe-korafe

Tuni dai kasashen duniya da dama suka yi Allah wadai da matakin da Isra'ilan ta dauka.

Kwamitin Sulhu na majalisar dinkin duniya ya yi kira da agudanar da bincike dangane da abinda ya faru a yayinda kwamandojin Isra'ila suka kaiwa jirgin ruwan mamaya a cikin teku.

Tuni itama kungiyar fafutukar kare hakkokin bil adama ta majalisar dinkin duniya ta amsa wannan kuwwar, wadda kuma tuni ta fara duba yiwuwar nemo gaskiyar.

Sai dai kuma Isra'ila bata dauki kungiyar fafutukar kare hakkokin bil adaman da mahimmanci ba, domin dai itace ta dauki nauyin wani bincike kan abinda Israelan tayi a zarin Gaza a shekarar 2009.

Isra'ila dai a lokacin taki bada goyon bayanta ga binciken, kuma akwai yiwuwar maimaita haka a binciken abinda ya faru yanzun.

Kasar Turkiyya dai na da mahimmiyar rawar da za ta taka a wannan muhawarar.

Jirgin dai na tafiya ne karkashin tutar kasar Turkiyyan, kuma mafi yawan wadanda suka rasu ko kuma wadanda suka ji raunuka 'yan kasar ta Turkiyya ne.

Abin dai kam da Turkiyya tafi so shi ne na majalisar dinkin duniya ta aiwatar da bincike.

Rawar da Amurka za ta taka

Kuma Amurka na tsaka tsaki, duk da ta damu da ta samu tabbacin abinda ya faru, wannan wani batu ne da ya shafi kawayenta biyu.

Alamu dai na bayyana cewa gwamnatin Obama na so ne a bar wannan batun, domin Isra'ila tayi bincike da kanta tare da taimakon kasashen duniya.

Wata shawarar kuma da mataimakin shugaban kasar ta Amurka Joe Biden ya bayar, itace ta bari Isra'ila tayi binciken da kanta tare da taimakon wadanda suka shahara akan harkar bincike.

Ya dai yi misali da binciken Korea ta Kudu dangane da nutsewar jirgin yakinta a matsayin abin koyi.

Duk wani bincike da za'a yi dai sai ya samu amincewar kasashen duniya, duk kuwa da cewa Isra'ila bata ambaci irin binciken da za ta yi ba.