Wasu abubuwa sun fashe a jihar Bayelsa

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Image caption Jihar Bayelsa mahaifar shugaba Goodluck Jonathan ce.

Takun-sakar da ake yi ta siyasa a jihar Bayelsa, dake kudu maso kudancin Nijeriya na cigaba da daukar wani sabon salo, hakan ya biyo bayan tashin wasu bama-bamai, biyu a Yenegoa, babban birnin jihar, a daren jiya.

Daya daga cikin bama-baman ya tashi ne a kusa da gidan mataimakin gwamanan Jihar Mr Peremobowei Ebebi, na kashin kansa, yayinda guda kuma ya tashi a kusa da wani Otel dake birnin.

Kwamishinan 'Yan sandan Jihar Bayelsa , Mr Onua Udeka ya tabbatar da tashin bama baman, ya kuma ce ba'a samu asarar rayuka ko jikkata ba.

Haka kuma, ko a jiya dai an cigaba da ja-in-ja a wani yunkuri da wasu 'yan majalisar dokokin jihar ta Bayelsa suka fara shekaranjiya na tsige mataimakin gwamnan daga kan mukaminsa.