Bama bamai biyu sun tashi a Bayelsa

Taswirar Najeriya

Rahotanni daga jihar Bayelsa da ke yankin Niger Delta a Najeriya na cewa bama bamai biyu sun tashi a daren ranar Laraba a Jihar.

Jihar Bayelsa ita ce dai mahaifar Shugaban Najeriya, Dokta Goodluck Jonathan.

Daya daga cikin bama baman dai ya tashi ne a gidan mataimakin gwamnan jihar Mista Peremobowei Ebebi, wanda a lokacin ba ya gidan na sa.

Bam na biyu kuwa ya tashi ne a a wani hotel mallakin mataimakin Shugaban majalisar dokokin jihar, Nestor Ibinabo wanda rahotanni suka nuna cewa yana goyan bayan gwamnan jihar Timpreye Slyva.

Babu rayukan da aka rasa a tashin bama baman biyu, amma hukumar 'yan sandan jihar ta ce tana ci gaba da bincikan lamarin.

Babu wata kungiya kawo yanzu da ta dau alhakin kaddamarda harin.

Ana dai samu rashin jituwa tsakanin gwamnan jihar da mataimakinsa, kuma a ranar Talatar da ta gabata ne majalisar dokokin jihar ta turawa mataimakin gwamnan takardar tuhumar tsige shi.

Gwagwar mayar siyasa

Masu lura da al'amura na ganin wannan rikicin yana da alaka da siyasa, a daidai lokacin da zabukan shekara ta 2011 ke karatowa.

Jihar Bayelsa dai ta dade tana fama da rikici daban daban, kama daga na siyasa da kuma na masu fafutukar samawa yankin 'yanci.

Har ila yau wasu na ganin rikicin na baya-bayan nan ba zai rasa nasaba da takun sakar da ake yi tsakanin gwamna Timipreye Slyva da kuma shugaban Najeriyar Dakta Goodluck Jonathan ba.

Rikicin wanda masu lura da al'amura suka ce ya samo asali ne lokacin da Mista Jonathan ke matsayin mataimakin shugaban kasa, da kuma abubuwan da suka biyo baya lokacin rashin lafiyar marigayi shugaba 'yar'adua.