An tsinci gawar Floribert Chebeya a Congo

Congo
Image caption Taswirar jamhuriyar damukradiyar Congo

An tsinci gawar wani sanannen mai fafutukar kwaton 'yancin bil Adama a kasar Congo wato Floribert Chebeya, a wajen babban birnin kasar na Kinshasa.

An tsinci gawar Mista Chebeya, wadda aka dan lullube ta da kaya, a bayan kujerar motarsa.

Wakilin BBC a Congon ya ce Mista Chebeya ya sha fama da cin zarafi daga 'yan sandan kasar congon a baya.

Haka kuma an shirya cewar zai bayyana a gaban shugaban 'yan sandan kasar a ranar Talata.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International dai tuni ta bayyana damuwarta game da mutuwar sanannen mai fafutukar inda tace ta ji takaici da kyamar yanayinda mai gwagwarmayar kare hakkin bil adaman ya rasu.