Daruruwan Palastinawa na hanyar Turkiya

Masu zanga zangar kin jinin Israila
Image caption Masu zanga zangar kin jinin Israila

Mutane fiye da dari hudu da hamsin dahudu ne masu gwagwarmayar kwato yancin Palasdinawa, da Israela ta fitar da su daga yankinta, bayan auka masu da ta yi a lokacinda suke kan hanyarsu ta zuwa Gaza a ranar litinin, a halin yanzu suka tashi zuwa kasar Turkiyya.

A lokacinda suka isa Istambul, wasu daga cikin masu fafutukar sun ce sun yi kokarin kare kansu ne daga dakarun Israela dake rike da manyan makamai.

Wakilin BBC ya ce wasu daga cikin masu gwagwarmayar sun fito daga jirgin suna daga tutar nasara, wasu kuwa sun fito ne daga jirgin da tabbuna da bangeji, sakamakon gamuwa da dakarun Israila da suka yi.

A bangare daya kuma wani jirgin ruwa na kan hanyarsa ta zuwa Gaza domin kokarin karya shingen da Israil ta kafa a yankin Gaza na Palastinawa.

Sai dai Israila wacce take da ikon yankin iyakokin ruwa na Gaza ta ce ba za'a kyale jirgin ruwan ya ketara ba.

A ranar litinin dai akalla mutane tara ne suka rasu a lokacinda sojin ruwan Israila suka far ma wasu jiragen ruwa dake dauke da kayan agaji ga Palasdinawar Zirin Gaza.