Cigaba a yunkurin dakatar da tsiyayar mai a tekun Mexico

Malalar mai a tekun Mexico
Image caption Malalar mai a tekun Mexico

Kamfanin mai na BP ya ce yana samun cigaba a kokarinsa na toshe bututun man da yake tsiyaya a karkashin teku a yunkurin dakatar da malalar man a tekun Mexico.

Injiniyoyi sun ce za su yi amfani da wata dabara wajen takaita yadda tsiyayar take gudana a kan bututun man.

Babban jami'in kamfanin na BP Tony Hayward ya ce za su fahimci ko za su sami nasara a yunkurin nasu, nan da sa'o'i ashirin da hudu. Wakilin BBC ya ce shugaba Obama zai kai ziyara ta uku gabar tekun a gobe.

Ya ci gaba da cewa idan yunkurin kamfanin ya yi nasara, to za su kawar da man dake tsiyaya zuwa cikin wani jirgin ruwan dake saman tekun.