Anyi jana'izan 'yan Turkiyyan da Isra'ila ta kashe

Hoton jana'izan 'yan Turkiyya
Image caption Turkiyya ta bukaci ayi cikakken bincike kan afkawa jiragen agajin da Isra'ila tayi.

A Turkiyya, anyi jana'izar wasu mutane tara masu fafutukar kare hakkin Palasdinawa da sojin kundumbalar Isra'ila suka kashe, bayan afkawa jiragen ruwansu dake kokarin kai kayan agaji a Zirin Gazar da Isra'ila ta datse.

Har yanzu ba a cimma daidaito ba game da irin nau'in binciken dalilan da suka sa sojojin kundumbalarta suka kai wannan harin. A yanzu haka dai Isra'ilar ta yi watsi da kiran a gudanar da binciken daga waje.