Nuhu Ribadu ya Koma Najeriya

Nuhu Ribadu
Image caption Nuhu Ribadu ya yi kaurin suna wajen yaki da cin hanci da rashawa

Tsohon shugaban Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ta Najeriya, Mallam Nuhu Ribado ya koma kasar.

Yau kusan sama shekara guda kenan ya shafe yana gudun hijirar sa-kai, kuma watanni biyu ke nan bayan an janye wata karar sa da aka yi bisa zargin cewa bai bayyana kadarorin da ya mallaka.

Tun aranar Alhamis ne ya sanar a shafin sa na Facebook cewa zai koma kasar domin halattar bikin karramashi da wata jami'a za ta yi, inda za a ba shi digirin girmamawa. Mallam Nuhu Ribado ya samu yabo daga kasashen duniya dangane da rawar da ya taka wajen tsarewa da kuma kwace kadarorin wasu da ake zargi lokacin da yake shugabantar Hukumar EFCC.

Sai dai ya tara abokan gaba sakamakon binciken da ya yi a kan wasu manyan `yan siyasa.

A shekara ta 2007 ne aka sallame shi daga aiki bayan shugaba Umaru Musa `yar'adua ya karbi shugabancin kasar.

Kana daga bisani ya fice zuwa kasar Birtaniya da Amurka saboda zargin da ya yi cewa rayuwarsa na cikin hadari.