Isra'ila ta yiwa jirgin ruwan agaji kawanya

Máiread Corrigan-Maguire
Image caption Máiread Corrigan-Maguire, wadda ta taba samun lambar yabo ta Nobel, na cikin masu fafutukar

Wani jirgin ruwan da ya nufi Zirin Gaza da nufin keta killacewar da Isra'ila ta yiwa yankin ya ce jiragen ruwan yaki na Isra’ilan sun taso shi gaba.

Ana kyautata zaton jirgin ruwan, wanda mallakin kasar Ireland ne, na da tazarar mil talatin da biyar daga gabar Gaza a tekun kasa-da-kasa.

Tuntubar jirgin ruwan mai suna 'Rachel Corrie' na da matukar wahala.

To amma wadanda suka tashi jirgin daga kasar Ireland sun ce sun samu sakon i-mel daga mutanen da ke cikin jirgin cewa sojojin ruwa na Isra'ila sun yi musu kawanya.

Mutanen da ke cikin jirgin ruwan sun kuma ce an datse hanyoyin sadarwa na jirgin.

Jirgin dai na dauke ne da kayan agaji da kuma masu fafutuka da ke goyon bayan Falasdinawa su goma sha daya, cikinsu har da tsofaffin jami'an diflomasiyya da wata mai fafutukar tabbatar da zaman lafiya wadda ta taba samun lambar yabo ta Nobel, Máiread Corrigan-Maguire.

Samamen da Isra'ila ta kai ranar Litinin a kan wani ayarin jiragen ruwa dauke da masu neman a bude iyakokin yankin Gaza dai ya shafawa kasar bakin fenti a idon duniya.

Sai dai Isra'ilar ta sha alwashin ba za ta kyale wannan jirgin ruwan ya isa Gaza ba.

Su kuma wadanda ke cikin jirgin sun ce ba za su nuna turjiya ba idan sojojin Isra'ilan suka far musu.

Isra'ilan dai ta yi tayin aikewa da wadansu daga cikin kayayyakin agajin ta mota bayan an tabbatar cewa ba su kunshi wadansu kayayyaki da kungiyar Hamas ka iya amfani da su don sarrafa makamai ba.